ABNA24 : Kafar watsa labarai ta Saberin wacce ta dauki labarin ta kara da cewa;An ga hayaki yana tashi daga sansanin sojan sama na Amurka a kusa da filin saukar jiragen sama na Arbil babban birnin yankin Kurdistan na Iraki, bayan da wani makamin roka ta fada a kansa.
Tuni dai aka rufe dukkanin hanyoyin da suka nufi filin saukar jiragen saman na Arbil.
Wata majiyar ta ce an kai harin ne da jirgin sama maras matuki wanda aka makare da abubuwa masu fashewa.Ya zuwa yanzu an tabbatar da jikkatar sojan Amurka guda.
A wani labarin daga Iraki, an kai wani harin ta’addancin a yankin al-Habibah dake gabashin birnin Bagadaza.
Bayanan farko sun ce an kai harin na ta’addanci ne a cikin kasuwar yankin wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutum guda da kuma jikkata wasu 12 da kone motoci biyar.
342/